Wednesday, 13 July 2016

AMANAR AURE


 ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ Amanar Aure๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ”…45and46๐Ÿ”…

A hankali Ameelah ta fara bude idonta, momie na zaune gefenta tayi tagumi, ta miqe da sauri ta qarasa inda take!

Qarema dakin kallo Ameelah tayi kafin abinda ya faru da ita ya fara dawo mata a qwaqwalwa! A firgice ta miqe zaune, tasa hannu ta fizge qarin ruwan da akai matah sannan ta dora hannu akai ta fasa wata razananniyar qara, jikinta sai kyarma yake nan danan taa hada xufa tana wani irin kuka marar dadin saurare!

Su abba da hilal da suke zaune a waje sukaji karar ta da sauri suka nufo dakin..

Can muka hango momie maqale jikin bango ta dafe qirji cike da tsoro, daqyar ta iya bin bango har takai qofa nan suka hado da hilal da Abbah suna shrin shgowa tare da likita!

Momie kam bata bisu ba sai dai ta tsaya riqe da qofa, su Abbah suka qarasa inda take suna tambyarta meya faru? Sai mexai faru? Muryarta ko kadan bata fita! Sai wani zazzare edo take tana kallonsu, saikace bata sansuba, edonuwanta sunyi jajir, Har lokacin jikinta bai daina 6ari ba!

A tsorace likita ke mata gwaje2..
     Tashin hankali na hango muku sosae a fuskar hilal dasu Abbah, momie kam har ta fara kuka tana sambatu abinda ya qara qular da Abbah kenan!

Likita ya dade yana mata gwaje gwaje kafin ya fara musu bayani "gsky wannan aikin bana asibiti bne, rashin lafiyar Ameelah har yanzu mun kasa ganoshi, amma ina baku shawara kuje wuren malamai ku nema mata taimaka!

Momie ta dafe kirji tace "na shiga uku! Wannan wane irin ciwo ne, Allah wannan sammu ne aka mata, ture ne za'a mata, domin mu duk danginmu babu mai jinnu! Koma waye sai Allah ya saka miki!

Abbah ya watsa mata harara yace "don Allah ki shga goma ba uku ba, lafiyar 'yerki zaki nema ko kwasar ma kanki zunubi xaki tsayayi wurin zato?

Daukar Ameelah zamuyi mu koma da ita can gidanmu mu nema mata magani? Ta daga kai tana gurnanin kuka cike da tausayin 'yer tatah!

Na:- ♥Rabiatu sk msh da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ
[4/17, 12:55 AM]
๐Ÿ’ ๐Ÿ’ Amanar Aure๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ”…47and48๐Ÿ”…

Daga asibitin wurin wani babban malami mai bada taimako suka wuce, sun mishi bayanin abnda ke damunta malam yasa almajirinshi ya kawo mishi ruwa a kofi ya tofa mata addu'o'i a ciki sannan ya watsa mata a fuska, tai wani irin zabura ta fara ihu da kyarmar jikin, nan malam yaci gaba da mata ruqiyya!

Duk yanda yaso Ameela tayi magana ko kadan bata fita, bugu (duka) kam ameelah ta shashi duk ta qara fita hayyacinta! Gata fara fatar jikinta tayi jaa sosai da manyan borarai,
     Daqyar aka samu kafaffen Aljanin ya fita, nan ta kwanta ta fara nannauyan barci!

Hilal duk da yana namiji sai da ya zubda mata hawaye, ji yake kamar ya maida ciwon jikinshi saboda tsananin tausayin matarshi, momy ma kuka take cike da tausayi, wani duka akayiwa ameelah shi saita rufe ido, saboda ihun da ameelah keyi,
    Abbah ne ke qarfafa musu gwiwan basu haquri yana kwantar musu da hnkali! (Su Ameela kam anji jiki, ko wannan ya isheta darasin cin Amanar Aure??)

Tufafin dake jikin ameelah duk sun lalace,

Abbah ne yace ma hilal yaje ya dauko mata kayanta saboda daga nan idan tafarka gida zasu wuce da ita saita qara samun sauqi! Jikinshi a sanyaye ya tafi cikin tunanin halin daya bar Ameelah!

Sai da yaje gidanne ya iske a bude kamar yadda ya barshi, yananan ynda suka barshi, qafarshi yaji ya daki wani abu akasa, ya duqa wayar Ameelah ne ya dago yana dubawa kusan 9 miss calls.

Bai duba ko na waye ba yana shirin ajewa wani kiran ya qara shgowa! "HMM" yaga an rubuta, ya dauka ya kara a kunnenshi yana shirin magana.. Hmm ya rugashi!

Cikin tattausan murya yake magana "haba! Haba!! Haba!!! My Ameelah ni babu abnda zaki cemun, kinsan yanda na shaqu dake bzanso kimin nisa ba koda na qaramin lokaci ne, ya za'ay ki brni tun jiya ba chat ba waya? Yayi shru yana jiran abnda zatace.

Shikau hilal mutuwar tsaye yayi da waya a hannunshi, ko motsi yaa kasayi! HMM yaci gaba "ya zaki shru ki qyaleni masoyiyah? Kinsan irin son da nake miki ko kin daina sonah ne? Nasan hkanma bzai yiwu ba amma kimin magana ko zanji dadi a raina!

Shi kadai yake magana yana qara ma hilal quncin zuciyah! Shi da kanshi ya gaji ya kashe har lokacin hilal yaa kasa cire wayar a kunnenshi yayi tsaye kamar wanda aka dasa!

๐Ÿ”†kuyi haquri plz da rashin jinmu kwana biyu dabaku yiba, duk muna exam ne๐Ÿ‘๐Ÿป Masu neman na bayanma su mana uzuri plz๐Ÿ”†

Na:-♥Rabiatu sk mashi, da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ

No comments:

Post a Comment