, ๐ ๐ Amanar Aure ๐ ๐
๐ ๐ ๐ ๐
๐
29 and 30๐
Via OHW๐ฑ๐
Favorite food dinta yasaya mata tuwon amala da miyar yakuwa,
Zauna tayi ta gyara cikinta, taci saida ta koshi sannan tatashi, taje kichin ta wanke hannayenta tayi drooping din ledojin a dustbin,
Ta wuce dakinshi kai tsaye,
tatura kofar dakin tashiga sannan tayi sallama, a kwance tasamesa saman gado, dagashi sai singlet sai gajeren wando yayi shirin bacci,
Batare daya ko motsa daga kwanciyar dayakeba ya amsa mata sallamar.
Sum2 ameelah takarasa bakin gadon ta zauna tana facing dinshi,
Tayi gyaran murya tace " fushi kake dani mijina"
Baikulata ba hasalima juya mata baya yayi,
Sai abin yasoma bawa ameelah dariya domin tasan hilal bazai taba fushi da ita,.ba. ( a zuci nace "oooh shiyasa takecin Amanarsa. Dan taga yana sonta, da karfi naji an firgi biro daga hannuna, "idan kingaji da rubutun kibani naci gaba" Bro abdul yafada ransa a bace, na shagwabe masa fuska kamar zanyi kuka nace " haba dan Allah nina cemaka nagajine. Tunanin wani abu kawai nake" sai yace "to naji karbi amma karki sake" nayi murmushj na karbi biron naci gaba da rubutu" ...
*** ***
Ameelah takara matsawa kusa dashi, ta dora hannunta a bayansa, tasaukar da murya "Dan Allah my heart beat kayi hkr, nayi maka alkawarin baxan karaba insha Allah"
Hilal ya juyo yana murmushi suka hada ido, ameelah tamayar masa da amsar murmushinsa, sannan ta lumshe, a lokacin daya kama hannunta yana shafar tsakiyar, hilal yace "kinyimun Alkawarin baxaki karaba, to idan kika sake fah"
A hankali ameelah ta bude ido tace "kayimun duk hukunci daya dace dani"
Hilal yayi murmushi yace "to shikenan uwar yayana, Allah yakara bamu ikon hakuri dajuna"
ameelah ta amsa da murmushi "Ameen mijina"
Cikin wasa Hilal ya matse mata hannu, Ameelah ta saka ihu kadan,
dariya yayi sosai, yace "matsoraciya, sai raki"
Ameelah ta shagwabe fuska tana yarfa hannun "Allah ni saina rama, haka kawai zaka jimun ciwo dan kaga baikai karfin kaba"
Hilal yatashi zauna, ya kura mata ido yana murmushi " tohm kirama mana idan kinada karfi" ya daga mata edo,
ameelah tace " to mikon hannunka"
hilal ya mika mata hannu, ameelah ta rike hannun taje ta matse hannun yayi mata dabara yakara matse mata hannu ta kara saka ihu, dasauri ya sauko daga kan gadon yana dariya sosai, ameelah tatashi tsaye tayo kansa tana gunguni. "Allah ni bazanyi hakuriba saina rama duka biyun" tana kokarin karasawa gurinsa yana janyewa, hardai abin yazamo musu wasa...
(Toh nidai naja birona, da littafi nafita, nacewa mr smiles shima yafito mubar musu dakin domin wasar tafara karfin da dazan iya rubuta waba, wasan maaurata, dole muka fito mukabar musu daki, muka dawo falo muka zauna muna jiran sugama wasar mucigaba da rubutu, wasa2 abin har muka kusan awa daya ba labarin fitowarsu, abdul yace "ke tashi muje nina gaji da jiran wadan nan muje gidan su afham muje muga wace wainar ake toyawa, ban musa masa ba domun nima nagaji da jiran, fita mukayi muka lula garin gombe...)
*** ***
Katon hijab tasaka sannan takawo safa ta rufe kafafunta da hannayenta, kyankyawace duk da babu kwalliya a fuskarta, fuskarta mai cike da kamala, annuri, da kuma haske, ....
Wacece wannan.... (Na tambayi bro Abdul)...
Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles๐
[11:17AM, 4/3/2016]
๐ ๐ Amanar Aure ๐ ๐
๐ ๐ ๐ ๐
๐
31 and 32๐
Via OHW๐ฑ๐
AMAL kenan, yarinya mai hankali da natsuwa ga son addini, ta turo kofar falon tashigo, aneesah da Ammi suna zaune a falon amal tashigo, aneesah ta tashi tana murna ta rungume amal, Ammi datake gefe tana murmushi tana kallonsu, bayan aneesah tasaki amal,
Amal ta sukuyar tagaida Ammi,
Ammi ta amsa cike da jindadi, sannan tatashi tabar musu falon, bayan sun zauna,
Aneesah tace " ya ustaxiya, ke kullum kinrufe jiki da katon hijab saikicevwata matar aure dubi dan Allah duk zafin nan kinsaka safa"
Amal tayi murmushi wadda yakara bayya dimples dinta "eh naji, komai zaki fada kifada, addinin mu yasanar damu cewa duk ilahirin jikin 'ya macce al'aurace bayan fuskarta da kuma tafin hannunta, kingakoh yazama dole narika rufe duk wata al'aura datake jikina"
Aneesah ta tabe baki "aikuwa daman nasani ana fara miki magana zaki fara yiwa mutane wa'azi "
murmushi amal tayi ta girgiza kai tace "hmm ai yanzu duk duniya tazama daya gaskiya wuyar fadane da ita, ida kuwa ka kuskura kafada to yanzu za'a rika kiranka mai waazi, karfa kimanta a cikin suratul AHZAB aya ta hamshin da tara 59 Allah subhanahu wata ala yana cewa, " َูุง ุฃََُّููุง ุงَّููุจُِّู ُูู ِّูุฃَุฒَْูุงุฌَِู َูุจََูุงุชَِู َِููุณَุงุกِ ุงْูู
ُุคْู
َِِููู ُูุฏَِْููู ุนَََِّْูููู ู
ِู ุฌََูุงุจِูุจَِِّูู ุฐََِٰูู ุฃَุฏَْٰูู ุฃَู ُูุนْุฑََْูู ََููุง ُูุคْุฐََْูู ََููุงَู ุงَُّููู ุบَُููุฑًุง ุฑَّุญِูู
ًุง " O Prophet! say to your wives and your daughters and the women of the believers that they let down upon them their over-garments; this will be more proper, that they may be known, and thus they will not be given trouble; and Allah is Forgiving, Merciful" " Yaa kai Annabi! Ka cewa matan aurenka da 'ya'yanka da matan muminai su kusantar da qasa daga manyan tufafin dake a kansu. Wancan yafi sauqi ga a ganesu domin kada a cucesu. Kuma Allah ya kasance mai garafa ne mai jin qai"
Aneesah taja nunfashi tace "Allahu akbar, nidai yanzu kiyi hkr zanma zo kikoyamun irin wannan shigar taki, nima naxamo ustaxiya" takarasa maganar tare da makkale murya, aneesah taci gaba da cewa " yanzu dai kitashi muje nakaiki ki gaida yaya afham yana cikin dakinsa, domin nasan wurinsa kikazo"
Amal ta sunkuyar da kanta cike da kunya, aneesah tazo ta kama hannunta suka nufi dakin Afham"
Zaune yake a kan wata kujera datake cikin dakinsa sanye yake da yadi fari, wadda yayi shara2 sosai, daga nesa zaka iya hango singlet dinda kejikinsa, yayi matukar kyau, photon ameelah yake kallon yana murmushi..
Amal ce tafara shigowa cikin dakin tare dayin sallama "Assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabara katuh" complete ta cika sallamar, hakan yasa Afham ya chanza yanayin fuskarsa, domin yagane ko wace, tun a gurin sallamar,
Kamar bazai amsaba saikuma ya amsa ciki2,
Aneesah tace "to tunda munzo ni bari nakoma nashirya miki abinci kafin kifito"
Cike da kunya Amal tace toh shikenan"
Nan aneesah tafita tabar musu dakin,
Shiru amal tayi tana tunanin mezata cemasa..
Maganar sace ta katse mata tunani, cike da bacin rai yace "lafiya meya kawoki dakina"
Amal tace "gaisawa kawai naxo muyi"
Afham yace " to shikenan mungaisa, saiki tafi koh"
Amal tayi gyaran murya tadaga edo ta kallesa, a ko wane bugun zuciyarta kara son afham take, amma tarasa dalilin dazaisa ya tsaneta,
Amal tace " ya Afham meyasa kake wulakantani, nifa mutumce kamarka, kuma yar adam kamarka amma narasa dalilin dazaisa karika wulakantani, dan Adam fa abin karramawane koda kuwa baka sansaba, balleni danake yar uwar, Allah subhanahu wata'ala yana cewa nakarrama dan adam fiye da kowace halinta datake doron duniya, yaya Afham kasani cewa..."
Afham yadaga mata hannu ransa abace, "ya isa haka, naji kuma nayarda, matsalar ki kenan daga anfara magana sai kifara wa'azi, ni ko wannan wa'azin naki yana daya daga cikin abubuwan da banaso, saikace wacca aka haifa agaban littantanfan islamiya, Afham yakara kallon irin yanayin shigar Amal, yaja tsaki yace "lok amal nifa tsarinki kwata kwata baimunba, ke gabaki daya local ce baki wayeba" yatashi tsaye yana nuna mata dan yatsa kamar zaikai mata duka "dubi yadda kike shigarki saikace yar gafaka, dan Allah Amal ki hakura dani, kinji ance kwarya tabi kwarya kibarni nasamu daidaini kema kije kisamu daidai ke"
Amal hawaye take sosai, tana danasanin zuwa dakinsa datayi, daman tasan wulakancine tukwauicin dazata samu, dolece tasa tazo saboda son datake masa,
Yaja tsaki yanufi hanyar fita, a bakin kofar yaci karo ammi dasauri yaja da baya, ammi takarasa shigowa dakin ta kalli amal sannan tajuya ta kalli afham ta bata rai sosai tace "daman nasan za'a rina, hakan yasa nabiyo bayanta domin nasan halin wannan bakar zuciyar taka, inajin duk irin abubuwan dakake fada mata, ka kyauta mutumen bazan, wadda bayajin maganar iyayensa"
Afham yakara tsuke fuska yana gunguni yace " yanzu ammi saboda amal zaki cemun mutumen banza" cike da hargowa ammi tace "eh nace, maras kunya wadda baya tsoron fushin iyayensa"
"To shikenan, afham yafada cike da bacij rai yanufi hanyar fita da karfi yaja kofar kamar zai karyata, yafita yana huci yabar dakin"....
Na:- ❤ Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles๐
No comments:
Post a Comment