Wednesday, 13 July 2016

AMANAR AURE

 ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ Amanar Aure
            ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
              ๐Ÿ”…33 and 34๐Ÿ”…

Via OHW๐Ÿ“ฑ๐Ÿ“š

kai tsaye garden ya wuce cike dajin haushin Amal, wayarshi ya fiddo yana addu'ar Allah yasa Ameelah na online ko fira suyi ya samu natsuwar zuciyarshi,

Cikin rashin sa'a kuwah bata online tsaji yaja, ya tura wayar cikin aljihu sannan ya lumshe ido, kamannun ameelah yafara bayyanowa a cikin zuciyar yana murmushi, tunanin ameelah kadai ya isa yasaka shi farin ciki,
        *** ***
Sai bayan la'asar lis sannan hilal yafita, bayan duk mai wakana ta auko tsakaninsa da matarsa ameelah, sabon wanka yasake tare sukayi wanka shida ameelah, yaudaikam yasamu farin ciki sosai a gurin ameelah, basu fito daga bandakinba saida sukayi alwala, suna fitowa hilal yajasu sallah, bayan sungama yafita...

Ameelah tafita tarakashi har waje, sannan tadawo cikin Falo yanayin Falon ta kalla yadda yayi kaca kaca, tayi ajiyar zuciyah, sannan tashiga gyara, komai batayi acikin gyaranba taji wayarta tayi karar shigowar text, da sauri ta ajiye aiki tanufi wuri wayar,

Sakon afham tagani, magiya yake mata akan dan Allah ta hau online, yayi miss dinta,

Murmushi kawai ameelah tayi, ta janyo data ta bude tana jiran shigowar massages,
          *** ***

 Afham yana zaune yaganta online wani dadi ya kama zuciyarshi don yanason chart da Ameelah, nan take ya manta da bacin ranshi cikin nishadi yake mata typng..

Afham "Ina fatan kyakkyawar mace ma mallakiyar zuciyatah tana cikin qoshin lpy.

Murmushi Ameelah tayi cike dajindadi

Ameelah "lpylau kaipa?

Afham " ina cikin Annashuwa dajin dadi, Ameelanah yau babu wanda ya kaini farin ciki, gsky nazo duniya cikin sa'a dana hadu dake๐Ÿ˜˜

Ameelah " 'nima nayi sa'a kuma ina cikin farin ciki"

 Afham "kinsan me? Inanan zaune nake a garden ganyayyakin itatuwa sai kadawa suke ga daddadan iska mai dadin shaka, ji nake dama muna tare! Don Allah Ameelah yaushe zamuyi aure??

Ameelah tazare ido, kafin tayi ajiyar zuciya

Ameelah "da wuri haka? Duka yaushe na sanka? ko soyayya bmu fara bapa"

Afham yayi murmushi, yana kallon text din ameelah azuci yake fadan, da ameelah tasan yadda yadamu dasuyi aure da wuri dabata fadi hakanba, kodan yabakan tawa amal zai nemi auren ameelah da wuri, bayan yadawo duniyar tunanin daya shiga yafara typng...

Afham "miye a cikin soyayyah Ameelah? Zamu dinga chart ne ko waya, kullum tambyr bazata wuce ya kke? Kinyi mafarkina? Gsky hotannan kinyi kyau sosae! Hmm wannan bashine soyayyaba, ni Kullum burina in kasance tare dake, amma sai dai ayita musayar kalamai ana bayyana shauqi, mezai hana muyi aurenmu kawai?

Gaban Ameelah ya fadi, lallai Akwai rigima, tana cikin tunanin text dn Afham ya kara shigowa
    Yace "son gaskiya nake miki Ameelah sona aure, idan kina ganin biki sanni ba ko banyi miki ba zan miki bayanin komi a kaina ga hotunanah nan, don Allah Ameelah ki zamo tawah karki gujemin!

Ajiyar zuciah tayi bayan ta gama karantawa duk ta hada zufa, hotunanshi ne take kallo ta jinjina kai a fili tace gaskia Afham kyakkyawan gaskene!

Yayi matuqar burgeta, nan tafara saqe saqe a zuci, ji take daman Afham ta fara haduwa dashi kafin ta auri hilal,

Na:- ♥Rabiatu sk mashi da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ
[4/7, 1:18 AM]
 ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ Amanar Aure๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
             ๐Ÿ”…35 and 36๐Ÿ”…

Via OHW๐Ÿ“ฑ๐Ÿ“š

Ranar sunyi chatn sosae da Afham ana shirin yin sallar magrib yasauka yace itama taje tayi sallah, amma taji har akayi sallar magrib tana zaune, sai bayan angama sannan tatashi tayi sallar, bayan tagama tana tatashi tadauki wayarta tasaka chaji amma ta gagara ajiye wayar sai duban DP din frds dinta take har lokacin da hilal ya dawo babu Abnda Ameelah tayi, sai da taji tsayuwan motarshi ta ajiye wayan da sauri ta fara gyaran dakin...

Da leda ya shigo a hannushi ta amsa ta mishi sannu da zuwa ya qarema dakin kallo yanda ya barshi haka ya iskeshi, tana shafar kai tace "tunda ka tafi nake bacci ban samu nayi komai ba gidan!

Hilal yiyi murmushi
    Yace "ay kara ki dinga hutawa, bari in fito in tayaki shara! Tayi murmushinta ya shge bedroom dinshi shima babu abnda ta gyara, haka ya shga toilet watsa ruwah shima ko wanki babu (sis rabi'at itama datake macce saida tace wannan wane irin jarabar chatn ne? Wasu matan zasuyi chatn bzasu gyara gdansu ba, babu ruwansu da tsaftar yaransu ko girkin mai gida! Sun gwammace su hau chatn suna cin Amanar aure, ko kuma chatn da qawayensu yaafi musu, nace "gsky ne ba duka matan ke da wannan tunanin ba)

Cikin sauri tashiga gyara gidan kafin ya fito, bayan yafito yazo yatayata suna aikin suna fira babu jimawa suka gama, ana kiran salar isha, hilal yafita yaje masallaci,

Yana fita, kamar tana jira, dasauri takoma gurin wayarta, daman datarta abude take, sakon ni taga sunshigo da yawa, harda wata bakuwar number, ta tsaya tana kallon number, number kamar bata Nigeria ba, saidai kuma hello kawai akace acikin number, saida ameelah takarewa number kallo sannan tafito, lambar hmm tagani ya auko mata sako, tayi sauri tashiga taduba, yace "beauty nayi miss din kalamanki dan Allah muhadu shabiyun dare akwai wani kyankyawan albishir dazan miki, plx kihau karki cemun kin manta saimun hadu" tayi ajiyar zuciya, kafin tafara zancen zuci "yanzu yazaayi muhadu, inason naji albishirin nan nasa" saikuma ta kada kai tace yes natuna,(na kalli rabi at nace "sis mekuma ameelah ta tuna ", tace "oho.. Musa ido mugani" nace "tomh)

Tana zaune tatuna da sallah dasauri tatashi tanufi bandaki bayan tafito tafara sallah, kamar wadda aka saka yin dole shaf shaf takarasa, tatashi ta nade sallayar sannan tafara shirin bacci kafin hilal yadawo,

Bayan ta kammala shirinta tafesa turare, sannan takoma kan gado ta kwanta, tanajiran dawowar hilal,

  Kusan mintinta ashirin a kwance tana jiran dawowarsa, jitayi anturo kofar dakin, tunkafin yakarsa shigowa tayi saurin gyara kwancinta, sannan tarufe ido, tafara jan minshari.....

Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ

No comments:

Post a Comment