Wednesday, 13 July 2016

AMANAR AURE

AMANAR AUREAmanar Aure๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
    ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 

            ๐Ÿ”…25 and 26๐Ÿ”…

Ameelah ta dafe kanta kafin ta yarfar da hannu tace "tohm miye ma A cikin Soyayyar? Soyayyah ne pa kawai shi da yake gombe ma ina xai ganni?" A zuci tayi maganar sannan ta buda datar ta taci gaba da charting dinta, amma a lokacin afham baya online, batama shiga Whtsapp ba Facebook tashiga tayi chart da dan fim..

 Akayi sallar laasar duk tana zaune, charting yahau kanta,
   (Wa'iyazubillah, wannan jarabar chart da masifa take, yanzu Ameelah ko tunanin mutuwa batayi, hmm Allah yakara karemu da kariyarsa, wai kaga mutum ana sallah shiyana zaune yana charting, wai bayason sauka, to idan baisauka anan duniyaba ai ya sauka kiyoma, Allah ya kyauta)
        *** ***
Har lokacin dawowar hilal yayi babu Abinda tayi tana kwance falo saman kujera ya shigo da sallamarshi da sauri ta ajiye wayar tana kallonshi kamar marar gaskiya sannan ta mishi sannu da zuwa..

Ya amsa a gajiye, ganin yanayinta yasa baikara maganaba ya shige dakinsa, dasauri ta janyo wayarta ta rufe data, tayi ajiyar zuciya, tana zaune ya fito ya zauna saman kujera ya kishingida, Yace "wlhy yau na gaji da yawa, ga yunwa da nakeji"

   Ameela ta dubesa tayi murmushi Tace "ayyah sannu"

 Hilal yace "sannu bazata gamsar da yunwar danakejiba ki daukomin Abncinah inci"

    cike da mamaki ameelah Tace "Yau kuma?

Hilal Yace "ban gane yau kuma ba?

Ameela takara yin murmushi Tace "naga ko breakfast baka tambayana ne, Yau kuma harda tambyar Abncin rana ko ka manta satin daya daka bani, baifa cikaba saura kwana biyu??

Girgiza kanshi yayi cikin takaici yaja tsaki, sannan ya daure ya danne damuwarshi ya tashi tsaye ya koma daki, ciki minti biyar ya fito ya canja shiga da mukullin motah a hannunshi, Yanufi kofar fita, tana zaune tana kallonsa,

Har yakai bakin kofa bai ce matah komi ba,
   sai itace tace "ina kuma zakaje?

Hilal Yace "zan fita ne inciyo abincin waje, tunda nayi aurenma bazan huta ba"

 Muryarta a shagwabe kamar zatayi kukah tace "ayni daman baka damu da cin abincinah ba"

murmushi hilal yayi yace "hmm ki fadi Abnda kike bukatah zan zo miki dashi, domin nasan kema yunwar kikeji"

Mikewah tayi tsaye sannan tace "ni sai dai ka tafi dani"

 cikin mamaki yake kallonta kafin yace "ina zakije ko sati bakiyi da aure ba? Ina zanbarki ki fita wani ya kallemunke, Kiyi zamanki ki huta, kinji"

   sororo tayi a tsaye don tasan maganace ya gaya matah, tana tsaye har yayi ficewarshi.

Ta tabe baki ta zauna taci gaba da chating dinta, kusan minti biyar tana jiran Afham har a lokacin bai hau ba, ta kagara suyi chart, ta rufe datar domin duk taji chart din ba dadi, ta ajiye wayar akan kujera, "Allah tadani naje nayi sallah" tafada sannan tatshi tanufi dakinta tashiga bandaki, tayi alwala sannan tafito tafara sallah, tayi raka'a biyu, tana cikin tahiya, taji karar wayarta a falo, a dai dai lokacin Hilal yashigo falo, da ledojin abinci a hannunsa, Ya dallawa Ameelah kira, saida ta zabura duk da sallah take, gabanta yayi mummunan faduwa,
    Yau kam asirina ya tonu" tafada a zuci...

Na:-♥ Rabiatu sk msh da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ
[7:06PM, 5/23/2016] Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ: [8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ: [6:16PM, 4/2/2016]
 ๐Ÿ’ ๐Ÿ’  Amanar Aure ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
            ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ ๐Ÿ’ 
           ๐Ÿ”…27 and 28๐Ÿ”…

Via OHW๐Ÿ“ฑ๐Ÿ“š

Jitayi anturo kofar dakin da karfi, duk inda ilahirin jikinta yake yadau rawa, tayi matukar tsorata,
   Hilal yashigo yatsaya yana kallonta tana sallah, ya girgiza kai ransa a bace yaja tsaki yafita ya koma falo,

   Jitakeyi kamar takarawa sallar gudu, shaf2 ta gama sallar ko adu'a bata tsaya yiba tafito falo a gigice,
   Wayarta tagani a hannun hilal, ta zare ido ta zabura kamar anmata sock, tayi matukar razana, taku takeyi cikin sanda ta sunkuyar da kanta kasa,
  Jin tafiyarta yasa hilal yajuyo sukayi ido hudu taga yanayinsa ya chanza, ta tsaya cak guri daya tana jiran taji mezaice
  A zuci take fadan nashiga ukku yau ruwa yakarewa dan kada"
   Ameela ! Hilal ya kirata,
   Cike da fargaba murya na rawa ta amsa,

 hilal yace "karaso nan" ya nuna mata kujera da hannunsa,
   Kafafuwanta har wani rawa suke dakyar takarasa bakin kujera tazauna, ta sunkuyar da kai tana wasa da dan yatsan, gabanta naduka shida shida,

   Hilal yadubeta cike mamaki " ameelah kinbata wayonki a banza wlh, kin zalunci kanki, wane irin rudine shedan yamiki dahar...." Ameela ta katse masa magana da shakankiyar muryarta, kamar mai shirin yin kuka tace " dan Allah dee kayi hkr wlh..."
  Hilal yadaga mata hannu, idanuwansa sunyi jajir yace "banason naji komai daga bakinki, wannan laifin da kikeyi bani kika yiwaba Allah subhanahu wata'ala kike sabawa, hilal yalura da irin tashin hankalin da ameelah take ciki, hawaye suka soma sauka kan kumatunta, yadan tsayar da maganar sa yana kallonta kafin yaci gaba dacewa "meya hanaki sallah da wuriii"

  Dasauri ameelah tadago kai tallesa, zuciyarta harwani sanyi tayi, tace
   Dee wlh bacci nake, koda natashi time ya wuce, amma kayi hkr bazan karaba"

  Ajiyar zuciya yayi ya tashi tsaye, sukayi ido hudu yace " laifinki biyu kenan kinyi karya a yanzu kuma kinkiyin sallah da wuri, ameelah matukar kinason muzauna lfy dake a cikin gidan nan to karna kara ganin kinyi late din sallah", mika mata wayarta yayi kafin yaci gaba da cewa "karbi wayarki naxo naga ana kira, kafin nakarasa gurin wayar kiran ya tsinke, wata number mai suna Hmm"
Cike da firgita ameelah tace " ehhhm"

hilal yakara kallonta "eh amma bansamu daukaba koda na naxo ta tsinke"

ya mika mata wayar sannan yajuya yanufi dakinsa,

  Wata irin babbar ajiyar zuciya tayi, ta share hawayen dake edonta, yana shigewa daki tadaga hannu sama "Allah nagodema "
   Tana gama fadan hakan ta sauka daga kankujera ta zauna kasa. Ta janyo ledar abinci tafara budewa...

Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles๐Ÿ˜ƒ

No comments:

Post a Comment